Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Navarro da ya daina bata sunanta kan COVID-19
2020-03-31 20:58:43        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bukaci mashawarcin fadar shugaban kasar Amurka kan harkokin cinikayya Peter Navarro da ya daina bata sunan kasar Sin kan COVID-19 da ma kokarin lalata alakar kasa da kasa.

Madam Hua ta ce, kullum kasar Sin tana gudanar da harkokinta ne ba tare da wata rufa-rufa ba, da ma sanar da hukumar lafiya da duniya (WHO) da kasashen duniya kan abin da take yi, ciki har da raba yanayin halittar kwayar cutar a kan lokaci tun lokacin da wannan annoba ta barke.

Haka kuma kasar Sin, tana shiga hadin gwiwar kasa da kasa don yaki da wannan annoba, sannan kasarta ta taimakawa bangarori daban-daban tare da samar da taimako ga wasu kasashe.

A baya-bayan nan ne dai, Navarro ya zargi kasar Sin yayin wata hira, inda ya ce wai ta mayar da kasashen duniya baya na tsawon makonni shida, saboda rashin fadawa sauran kasashe cewa, wani yana iya yada cutar COVID-19 ga wani, zargin da mahukuntan kasar ta Sin suka yi Allah wadai da shi.

Madam Hua ta ce mece ce manufar dan siyasar ta Amurka? Abin da ya ke nema shi ne jirkita gaskiya, ya kuma dorawa wasu laifi, da lalata alakar Sin da Amurka kan yaki da wannan annoba, da ma hadin gwiwar kasashen duniya a wannan fanni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China