Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Kamata ya yi a gaggauta farfado da kanana da matsakaitan kamfanoni daga illar COVID 19
2020-03-30 11:24:38        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci lardin Zhejiang a jiya Lahadi, inda ya tattauna da wakilan kanana da matsakaitan kamfanoni, a cibiyar ba da hidimma ta sansanin sayar da kayayyakin motoci dake unguwar Daqi, na yankin Beilun dake birnin Ningbo.

Xi Jinping ya ce, COVID-19 na illata kamfanoni daban-daban, saboda ganin haka, kwamitin tsakiya na JKS na mai da hankali sosai kan kanana da matsakaitan kamfanoni, kuma ya riga ya gabatar da jerin matakai masu inganci, kuma zai gyaran fuskar wadannan matakai bisa halin da ake ciki, don kawar da illar da cutar ke yiwa wadannan kamfanoni, ban da wannan kuma, za su samu sabon ci gaba. Ziyarar shugaba Xi Jinping a wannan karo na da burin sauraron ra'ayin jama'a. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China