Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane fiye da miliyan 2.8 sun bar lardin Hubei don dawowa bakin aikinsu
2020-03-30 11:19:12        cri

A 'yan kwanakin nan ne aka kawar da matakin hana fitowa daga lardin Hubei da ya fi fama da cutar COVID-19 a kasar Sin, inda kididdigar da lardin ya fitar ta nuna cewa, ya zuwa ran 28 ga watan nan, mutanen dake cikin lardin da yawansa ya kai miliyan 4.6 sun koma bakin aikinsu, daga cikinsu miliyan 1.8 na aiki a lardin, yayin da sauran miliyan 2.8 suka tafi zuwa larduna daban-daban.

Wuraren da wadannan mutane suka tafi sun hada da lardin Guangdong, da Zhejiang da Jiangsu da kuma Fujian da dai sauran wurare, dake dab da teku, da yankin arewa maso gabas. Daga cikinsu, yawan mutanen hadda kaso 40 bisa dari na daukacin matafi lardin Guangdong.

Wadanda suka koma aiki a lardin daga birnin Wuhan sun nuna cewa, yanzu zaman rayuwarsu na tafiya yadda ya kamata, ana yin aiki lami lafiya, kuma ana ci gaba da binciken zafin jiki a dakunan cin abinci da kuma ofisoshi, kuma abokan ma'aikata na maraba da su kwarai. A sa'i daya kuma, suna kokarin kandagarki, da rage fitowa waje, ko yin taruka, ko cin abinci tare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China