Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mene ne amfanin magungunan gargajiya na kasar Sin wajen yakar COVID 19?
2020-04-01 12:36:52        cri

Kwanan baya, kafar CGTN dake karkashin CMG ya gabatar da shiri na musamman mai taken "Dakin ba da jiyya na kasa da kasa", inda ya watsa wani shiri kai tsaye dangane da magungunan gargajiya na kasar Sin. Likitoci masana magungunan gargajiya ta kasar Sin wadanda suka samar da gudummawar jiyya a birnin Wuhan da kuma wadanda suka samar da jiyya ga masu harbuwa da cutar numfashi ta Covid-19 sun yi bayani ga takwarorinsu na kasar Amurka da Lebanon da kuma Afghanistan da Pakistan da kuma Iran, kan gudunmawar da magungunan gargajiya na kasar Sin suka bayar wajen yakar cutar COVID 19.

Shugaban asibitin maganin gargajiya na Beijing Liu Qingquan ya ce, an samar wa kaso 90% na masu cutar magungunan gargajiya na kasar Sin, magungunan da suka taka matukar rawa wajen hana shiga halin mutu kwakwai rai kwakwai, da kuma rage yawan mamata.

Masanin likitancin gargajiya na kasar Sin na jihar Colorado na Amurka Joseph Brady ya nuna sha'awa sosai kan wasu magungunan gargiya uku da aka yi amfani da su wajen yakar cutar, yana fatan likitocin gargajiya na kasar Sin su yi karin bayani kan sinadaran magungunan, don a yi amfani da su bisa halin da ake ciki a wurare daban-daban. Liu Qingquan ba kawai ya bayyana sinadaran da ake amfani da su wajen harhada magungunan ba, har ma ya yi bayyani kan amfaninsu.

Wannan taro ya kwashe mintoci 100, yawan mutanen da suka kalli shirin ya kai fiye da miliyan 1.54, haka kuma yawan masu kallon bidiyo ya kai dubu 489. Tun lokacin da aka gabatar da wannan shiri a ran 11 ga watan Maris, an yi taruruka 16 ta kafar bidiyo, inda mutane fiye da miliyan 59.84 suka kalli wannan shiri, yawan mutanen da suka kalli bidiyo ya kai miliyan 20.87. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China