Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba a samu sabon wanda ya kamu da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin ba
2020-03-31 11:23:37        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta bayyana a yau Talata cewa, ba a samu yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a cikin babban yankin kasar ba a jiya Litinin.

Sai dai, hukumar ta ce ta samu rahoton mutane 48 da suka shigo da cutar babban yankin kasar a jiyan.

A cewar hukumar, ya zuwa karshen jiyan, jimilar mutane 771 ne suka shigo da cutar kasar, daga ketare. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China