Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Australiya: Amurka ce babban asalin yaduwar cutar COVID-19 a Australiya
2020-03-22 17:09:01        cri
A ranar 1 ga wata, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 bai wuce 30 ba a kasar Australiya, amma sakamakon karin mutanen da suka shigo kasar gami da saurin yaduwar cutar tsakanin mutum da mutum, tun daga ranar 18 ga wata, adadin mutanen da aka tabbatar suna kamuwa da cutar a kasar yana kaiwa 100 ko ma fiye da haka a kowace rana. Kididdigar ta yi nuni da cewa, zuwa karfe 2 na yammacin jiya 21 ga wata, gaba daya akwai mutane 1073 wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ta Australiya.

Firaministan kasar Scott Morrison ya zanta da gidan rediyon 2GB a kwanan nan ya bayyana cewa, kimanin kaso 80% daga cikin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Australiya, sun shigo kasar ne daga sauran sassan duniya, ko kuma sun taba yin mu'amala kai-tsaye da wadanda suka shigo kasar daga ketare, kana, akasarinsu daga Amurka ne. Morrison ya kara da cewa, a ra'ayinsa, babu wata alamar dake nuna cewa duk wata kasa, ciki har da kasar Sin, ta aikata wani abu da gangan.

Kafofin watsa labarai da dama sun bayyana irin wannan furucin na Morrison a matsayin suka ga gwamnatin Donald Trump saboda sakacin da ta yi wajen dakile yaduwar cutar. Kwararru da masana daga bangaren lafiya da gwamnatin kasar Australiya sun nuna cewa, har yanzu ba a kai ga mataki mafi muni na yaduwar COVID-19 a Australiya ba. Kuma bisa hasashen da aka yi, zuwa lokaci mafi muni, za'a samu mutane miliyan 15 wadanda suka kamu da cutar, kuma yawan mace-macen da za'a samu zai iya kaiwa dubu 150, har ma za'a dauki akalla rabin shekara ana fama da annobar a kasar ta Australiya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China