Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Likitan Italiya ya ce mai yiwu an samu bullar kwayar cutar COVID-19 a arewacin kasar ne tun a karshen shekarar bara
2020-03-22 17:09:49        cri
Yayin da yake zantawa da kafofin watsa labaran Amurka kwanan nan, wani sanannen likitan kasar Italiya mai suna Giuseppe Remuzzi ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne an samun bullar cutar huhun da ake zargin cutar COVID-19 ce tun a watannin Nuwamba da Disambar bara a kasar.

Dr. Giuseppe Remuzzi shine babban daraktan cibiyar nazarin ilimin magunguna ta Mario Negri wadda ta yi suna sosai a kasar Italiya har ma a duk nahiyar Turai baki daya. A zantawarsa da kafar yada labarai ta National public radio ta Amurka, Dr. Giuseppe Remuzzi ya fayyace cewa, wasu likitocin Italiya sun gaya masa a kwanakin nan cewa, sun taba kula da wasu mutanen da suka kamu da ciwon huhu mai tsanani wanda ba'a saba ganin irinsa ba, musamman a wasu tsofaffi ne suka kamu da cutar tun a watan Disamba har ma a watan Nuwambar bara.

Dr. Giuseppe Remuzzi ya kara da cewa, kafin a lura da bayyanar annobar cutar COVID-19 da ta barke a kasar Sin, kwayar cutar ta fara bazuwa a yankin Lombardia dake arewacin kasar Italiya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China