Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fadada jigilar kayayyaki ta sama domin samar da isassun kayayyakin kiwon lafiya ga sassan duniya
2020-03-30 13:29:27        cri
A yayin da sassan duniya da dama ke fama da yaki da cutar numfashi ta COVID-19, yanzu haka kasar Sin ta fadada jigilar kayayyaki ta jiragen sama, domin samar da isassun kayayyakin kiwon lafiya da ake bukata, wajen cimma nasarar yaki da wannan cuta.

Yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Lahadi, Zhang Qing, jami'i a hukumar lura da sufurin jiragen sama na kasar Sin, ya bayyana cewa, a ranar Alhamis jirage sun yi sufuri 23 ta filayen jiragen sama na kasa da kasa, inda suka yi dakon kayan da yawan su ya kai Tan 406.

Shi kuwa a nasa tsokaci, babban jami'i a hukumar dake lura da aikewa da sakwanni ta kasar Sin Jin Jinghua, cewa ya yi duk da yake ana fuskantar karancin jiragen sama dake sufiri, da karancin hanyoyin aikewa da kayayyaki sakamakon barkewar wannan cuta, a hannu guda kasar Sin za ta ci gaba da jirage na shata, za kuma ta bude karin hanyoyinta na sama, don tabbatar da safarar kayayyakin da suka wajaba, da kayan bukatun lafiya ga sassan duniya daban daban. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China