Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba a samu sabbin mutanen da suka kamu da COVID-19 a Wuhan ba
2020-03-30 10:51:27        cri

A ranar Lahadin da ta gabata ba a samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Wuhan na kasar Sin ba, garin da a baya ya kasance wajen da cutar ta fi kamari dake lardin Hubei a tsakiyar kasar Sin.

Wata sanarwar da hukumar lafiyar kasar Sin ta fitar ta ce, a ranar Lahadin ba a samu rahoton sabbin mutanen da suka kamu da cutar ta COVID-19 a lardin ba.

A lardin na Hubei an samu sabbin mutane 4 da suka mutu kuma dukkansu a garin Wuhan. Ba a samu sabbin mutanen da ake zaton sun kamu da cutar ba a lardin a ranar Lahadin.

Kimanin majinyata 317 aka sallama daga asibiti a wannan rana ta Lahadi. Daga cikin majinyata 1,733 da ake kula da lafiyarsu a asibiti, 427 suna cikin yanayi mai tsanani kana 174 suna cikin yanayi mafi tsanani na fama da cutar.

Ya zuwa yanzu, lardin Hubei an samu jimillar mutane 67,801 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, wanda ya kunshi 50,006 a birnin Wuhan. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China