Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta bayyana takaicinta kan wasu kafofin watsa labaru 3 na Amurka
2020-03-28 17:05:57        cri
Jami'in sashen watsa labaru na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya gana da jami'an jaridun The New York Times da The Wall Street Journal da kuma The Washington Post dake nan birnin Beijing daya bayan daya a jiya, inda ya bayyana rashin jin dadi dongane da wasikun da suka rubutawa gwamnatin kasar Sin a kwanakin baya.

Bangaren Sin ya bayyana cewa, kasar ta dauki matakan da suka dace kuma bisa tushe, don mayar da martani kan matsin lambar da Amurka da ta dade t na yi wa kafofinta na watsa labarun dake kasar.

Bangaren Sin ya kuma jaddada cewa, ko da yaushe kasar Sin na maraba da 'yan jaridar kasashen ketare su gudanar da ayyukansu bisa doka da ka'ida a kasar. Amma abubuwan da kasar Sin ke adawa su su ne, rainata da ake yi da yada labarun karya bisa hujjar 'yancin watsa labaru, da kuma ayyukan saba wa da'ar sana'ar watsa labaru. Idan kafofin watsa labarun uku ba su ji dadin matakan ba, sai su bayyana korafinsu ga gwamnatin Amurka.(Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China