2019-08-09 10:51:31 cri |
Rahotanni sun ce hukumar kula da ayyuka ta Amurka, ta fitar da wani umarni na wucin gadi, wanda ya haramtawa dukkan hukumomin gwamnati sayar da kayayyakin sadarwa da bada hidimomi ga kamfanoni biyar na kasar Sin, ciki har da kamfanin Huawei, bisa dogaro da tanadin dokar kasafin kudi na hukumar tsaron Amurka na shekarar kudi ta 2019.
Da take amsa tambayar da manema labarai suka yi mata dangane da batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Hua Chunying, ta bayyana rashin gamsuwar kasar Sin da kuma adawa da dabi'ar Amurka, na nuna wariya da daukar matakan da ba su dace ba a kan wasu kamfanonin Sin, bisa wasu munanan bayanai kan kasar Sin dake kunshe cikin dokar kasafin kudin hukumar tsaron Amurkar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China