Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na maraba da sanarwar da Amurka ta fitar ta dakatar da sanyawa hajojin Sin haraji
2019-09-12 20:44:49        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, kasarsa tana maraba da sanarwar da Amurka ta fitar cewa, za ta dakatar da buga haraji kan hajojin kasar Sin.

A yayin taron manema labarai da aka shirya yau Alhamis, Gao ya ce, Sin na maraba da wannan kyakkyawan mataki da Amurka ta dauka. Ya ce akwai wasu kamfanonin kasar Sin wadanda suka fara tambayar farashin amfanin gonar Amurka, yana mai cewa, ma'aikatan tawagogin Sin da Amurka a tattaunawar tattalin arziki da cinikayyar za su gana nan ba da jimawa ba, don share fagen gudanar da shawarwari zagaye na 13 kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jami'an kasahen biyu.

Har wa yau, Gao ya ce, kasar Sin ba ta sauya matsayinta ba kan batun shawarwari, inda take fatan kasashen biyu za su ci gaba da hada gwiwa don kirkiro yanayi mai kyau ga shawarwarin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China