Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Sin za ta ba da gudummawarta wajen kiyaye ci gaban tattalin arzikin duniya
2020-03-26 21:54:17        cri
A yau Alhamis ne aka kaddamar da taron kolin G20 na musamman, kan batun yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron daga nan birnin Beijing.

A gun taron, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara karfin samar da magunguna, da kayayyakin masarufi, da na kandagarkin cutar ga kasuwannin duniya, za ta kuma tsaya tsayin daka a fannin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, tare da kyautata yanayin kasuwanci a kasar, da habaka shigowa da kayayyaki daga ketare, don samar da gudummawarta ga kiyaye tattalin arzikin duniya.

Har ila yau, ya jaddada cewa, cutar ta haifar da munanan illoli ga ayyukan samar da kayayyaki a duniya, don haka kamata ya yi kasa da kasa su hada kansu wajen daukar managartan matakai daga manyan fannoni, don hana tabarbarewar tattalin arzikin duniya.

Baya ga haka, ya kuma yi kira ga kasashen G20 da su dauki matakai na bai daya, su rage kudin kwastan, da kawar da shingayen ciniki, don farfado da tattalin arzikin duniya. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China