Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya yi kira da a dauki dukkanin matakan yaki da cutar COVID-19 a duniya baki daya
2020-03-26 21:54:56        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a dauki dukkanin matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a duniya baki daya, yana mai cewa abu ne mai muhimmanci ga kasashen duniya, su karfafa kwarin gwiwarsu, su hada kai, tare da aiki tare, domin dakile wannan annoba cikin hadin gwiwa.

Xi Jinping ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin da yake halartar taron kolin G20 na musamman, kan batun yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ta kafar bidiyo. Ya ce Sin ta karbi tallafi da karfafa gwiwa daga sassan duniya daban daban, a lokacin da take tsaka da fuskantar mawuyacin hali na yaki da cutar ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China