Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya halarci taron kolin G20 na musamman
2020-03-26 21:09:28        cri
A yau Alhamis ne aka kaddamar da taron kolin G20 na musamman, kan batun yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron daga nan birnin Beijing.

Kasar Saudiyya ce ta dauki nauyin shirya taron, kuma an gudanar taron ne ta yanar gizo. Kasashe mambobin G20, da kasashe baki, da kuma jami'an kungiyoyin kasa da kasa masu ruwa da tsaki sun halarci taron. Wannan ne karon farko da G20 ta gudanar da taron shugabanninta ta yanar gizo, haka kuma karo na farko da shugaban kasar Sin ya halarci babban taron kasa da kasa tun bayan barkewar cutar. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China