Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping zai halarci taro ta kafar bidiyo tsakanin shugabannin kasashen G20
2020-03-25 21:00:15        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci wani taro na musamman ta kafar bidiyo, game da lalubo bakin zaren daidaita annobar cutar COVID-19, na shugabannin kasashen G20 a gobe Alhamis a nan birnin Beijing.

Yau Laraba, mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Ma Zhaoxu, ya zanta da kafofin yada labarai, domin bayyana yadda taron zai kasance, da abun da kasar Sin ke fatan cimmawa. Ma ya ce, taron zai kasance karon farko da za'a yi shi ta kafar bidiyo tsakanin shugabannin kasashen G20, kana taron kasa da kasa na farko da shugaba Xi zai halarta tun bayan barkewar cutar COVID-19.

Ma ya ce, G20 muhimmin dandali ne na kasa da kasa, na tinkarar hadurra, da tafiyar da harkokin tattalin arziki, wanda ya kunshi muhimman kasashe masu karfin tattalin arziki, da kasashen dake tasowa.

A daidai wannan muhimmin lokaci, kiran taro na musamman kan batun dakile yaduwar cutar COVID-19 na G20 na da ma'ana kwarai da gaske, musamman a fannonin da suka shafi hana yaduwar cutar a duniya, da tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasa da kasa.

Game da abubuwan da kasar Sin take son cimmawa a wajen taron, Ma Zhaoxu ya yi karin haske da cewa, na farko, kara zama tsintsiya madaurinki daya. Kwayar cutar na iya bazuwa tsakanin kasa da kasa, babu wata kasa da za ta iya kebe kanta daga irin wannan masifa. Na biyu, inganta hadin-gwiwa, inda kasar Sin take fatan kasashen G20 za su yi taimakekeniya, domin kiyaye lafiyar al'ummar duk duniya. Na uku wato na karshe, zurfafa mu'amala tsakanin kasa da kasa. Kasar Sin na fatan bangarori masu ruwa da tsaki za su aiwatar da manufofin tattalin arziki da suka wajaba, da ci gaba da bude kofar kasuwa, a wani kokari na farfado da imanin kasuwannin duniya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China