Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta tsaurara matakan tunkarar barkewar cutar Corona
2020-02-15 15:59:43        cri

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Tarayyar Afrika wato Africa CDC, ta ce ana inganta matakan shiryawa yuwuwar barkewar cutar numfashi ta Corona a nahiyar.

Yayin wani taron manema labarai na mako-mako a hedkwatar Tarayyar dake Addis Ababa na Habasha, daraktan cibiyar, Dr. John Nkengasong, ya ce cibiyar na gudanar da tsare-tsare da ayyuka, kan yadda nahiyar za ta shirya tare da tunkarar yuwuwar barkewar cutar Corona.

Cibiyar wadda ta hada kwararru daga fadin nahiyar, daga kasashe 5 da suka hada da Senegal da Kenya da Morocco da Nijeriya da Afrika ta Kudu, za ta mayar da hankali kan fannonin 5 da za ta sawa ido, wadanda suka hada da matakan kariya da na dakile yaduwar cutar da jinyar wadanda suka kamu da bada bayanan hadduran da za a iya fuskanta da kuma kula da lafiyar al'umma. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China