Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi maraba da tsagaita bude da mayakan 'yan awaren Kamaru suka sanar
2020-03-27 10:06:23        cri
MDD ta yi maraba da sanarwar da mayakan 'yan awaren kudancin Kamaru (SOCADEF) suka bayar na tsagaita bude wuta, biyo bayan kiran da babban sakataren MDDr Antonio Guterres ya yi, na tsagaita bude wuta a duk fadin duniya, a kokakin ganin an inganta matakan da ake dauka a sassan duniya na ganin bayan annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Babban sakataren na MDD Antonio Guterres, ya kuma yi kira ga sauran kungiyoyi masu dauke da makamai, da su ma su dauki irin wannan mataki.

Guterres ya nanata kiran sake komawa kan teburin sulhu, don magance dukkan batutuwa masu muhimmanci a yankin arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar ta Kamaru, don kawo karshen tashin hankali da kuncin da jama'a ke fuskanta a wadannan yankuna.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China