2020-01-21 10:43:53 cri |
A Juma'ar da ta gabata, sojojin kurfau na Jamhuriyar Kamaru dake aikin sintiri akan iyakokin kasar sun damke wata motar bas da ake zargi a yankin dake makwabtaka da Equatorial Guinea. sojojin sun yi nasarar kama mutune uku da ake zargin, ciki har da wasu mata da miji da wani mai yin garkuwa, inda suka ceto yara kanana biyu da aka yi garkuwa da su, 'yan tsakanin shekaru 3 zuwa 10 da haihuwa.
Yaran biyu an yi garkuwa da su ne a ranar Alhamis din data gabata, wata mace mai matsakaitan shekaru ce ta yi garkuwar da su, kana ta amsa laifinta a lokacin da ake mata tambayoyi cewa wasu ma'aurata ne suka yi mata alkawarin biyanta kudi kimamin CFA 1,800,000 kwatankwacin dala 3,000 a kan yaran biyu.
Tuni aka sada yaran da iyalansu, kuma suna cikin koshin lafiya, kamar yadda jami'an tsaron suka tabbatar, jami'an sun kara da cewa, tuni aka kaddamar da shirin binciken a hukumance domin wargaza duk wani shirin hadin gwiwar safarar kananan yara akan iyakokin kasar. (Ahmnad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China