Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a gudanar da gasar cin kofin Afirka kafin lokacin da aka tsara
2020-01-16 10:44:13        cri
Hukumar shirya gasar wasan kwallon kafa ta Afirka ta sanar a jiya cewa, bisa yanayin da kasar Kamaru take ciki, an tsaida kudurin gudanar da gasar cin kofin Afirka daga ranar 9 ga watan Janairu zuwa ranar 6 ga watan Febrairu na shekarar 2021 a kasar kafin lokacin da aka tsara wato watan Yuni zuwa Yuli na shekarar.

Kasar Kamaru, wadda za a karbi bakuncin gasar ta bayar da shawarar canja lokacin gudanar da gasar cin kofin Afirka, saboda a watan Yuni zuwa Yuli na kowace shekara, lokaci ne na damina a yawancin yankunan kasar. Shugaban hukumar shirya gasar wasan kwallon kafa ta Afirka Ahmed ya kai ziyara kasar ta Kamaru tare da tawagarsa a ranar 13 ga wannan wata, bayan da ya saurari ra'ayoyin bangaren kasar Kamaru da yadda aikin gina filayen wasan ke gudana, ya amince da gudanar da gasar cin kofin Afirka kafin lokacin da aka tsara.

A sakamakon gaza gama aikin gina filayen da za a gudanar da gasar kamar yadda aka tsara, hukumar shirya gasar wasan kwallon kafa ta Afirka ta soke iznin kasar Kamaru na daukar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2019. Ahmed ya bayyanawa 'yan jarida a jiya cewa, hukumar ta yi imani cewa kasar Kamaru tana da karfin gudanar da gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2021 yadda ya kamata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China