![]() |
|
2020-02-10 13:05:12 cri |
Rundunar sojojin kasar Kamaru ta sanar cewa an kashe mayakan 'yan aware 7 a ranar Lahadi a lokacin da suka yi yunkurin kaddamar da hari kan rumfunan zabe a shiyyar kudu maso yammacin yankin Kamaru mai magana da yaren Turanci.
Lamarin ya faru ne a garin Bangem a lokacin gudanar da zabukan 'yan majalisun dokokin kasar da na kananan hukumomi wadanda aka gudanar a ranar Lahadi a kasar ta shiyyar tsakiyar Afrika. Zabukan da aka gudanar a karon farko tun bayan shekaru bakwai bayan jinkirin da aka samu har sau biyu.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China