Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mutane 5 da aka yi garkuwa da su, ciki har da magajin gari a Kamaru
2020-03-13 11:12:04        cri
Babban jami'in yankin Ngoketunjia na kasar Kamaru, Quetong Anderson Kongueh, ya bayyana a jiya cewa, 'yan a-ware na yankin arewa maso yammacin kasar mai rinjayen masu amfani da Turancin Ingilishi, sun kashe fararen hula 5 da suka yi garkuwa da su.

'Yan a-waren sun kashe mutane 4 da suka yi garkuwa da su, ciki har da mataimakin magajin garin yankin Babessi, Chefor Oscar, bayan sojojin sun lalata sansaninsu.

Haka zalika a jiyan, 'yan a-waren sun kashe sabon magajin garin yankin Mbengwi, Ndangsa Kenedy Akam, wanda aka sace kwanaki 15 da suka gabata.

A cewar jami'in, lamarin na jiya ya nuna cewa ana yakin neman 'yancin ne a kan al'umma, yana mai cewa akwai bukatar jama'a su kafa kungiyar 'yan banga tare da hada hannu da jami'an tsaron gwamnati domin ceton kansu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China