![]() |
|
2020-03-06 20:49:54 cri |
Gidan talabijin na kasar Kamaru CRTV ya ruwaito sanarwar ma'aikatar dake cewa, wanda ya kamu da cutar, wani dan asalin kasar Faransa ne, mai shekaru 58 a duniya, wanda ya isa birnin Yaounde a ranar 24 ga watan Fabrairu.
Sanarwar ta kara da cewa, an riga an killace dan Faransan don ba shi magani a babban asibitin Yaounde, kuma an bukaci al'ummar kasar su yi taka-tsantsan da mutunta ka'idojin kiwon lafiya.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China