Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta ba da shawara kan kyautata tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya a yayin taron kolin Osaka
2019-06-30 16:23:23        cri

Wang Xiaolong, wakilin musamman na kasar Sin mai kula da harkokin kungiyar G20,kuma shugaban sashen kula da harkokin tattalin arzikin duniya na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya shirya taron manema labaru a birnin Osakan kasar Japan a jiya, inda ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta ba da shawara kan kyautata tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya a lokacin taron kolin G20.

Mista Wang ya ce, a karshe taron kolin, kasashe mambobin kungiyar sun cimma daidaito kan batun sauyin yanayi, lamarin dake da amfani ga hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar kiyaye muhalli, da samun ci gaba mai dorewa, musamman ma wajen daidaita sauyin yanayi.

Haka zalika, mista Wang ya nuna cewa, kasashe mambobin kungiyar ta G20, sun cimma matsaya guda kan goyon bayan tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, inda aka sanya hukumar ciniki ta duniya wato WTO gaba da komai, wanda ya zama sharadi na farko na yiwa hukumar ta WTO kwaskwarima. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China