Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tabbatar da sabbin mutane 78 sun kamu da cutar COVID-19
2020-03-24 10:29:13        cri

Bisa kididdigar da hukumar lafiya ta kasar Sin ta yi, a jiya Litinin, karin mutane 78 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar, inda 74 daga cikinsu suka taho da cutar daga ketare. Ya zuwa jiya Litinin yawan wadanda suka taho da cutar daga ketare ya kai 427.

Haka kuma ya zuwa jiyan, jimilar mutane 4735 ne ke fama da cutar a babban yankin kasar Sin, yayin da mutane 73159 suka warke daga cutar, kuma aka sallame su daga asibiti, kana mutane 3277 sun rasa rayukansu. Jimillar wadanda suka kamu da cutar ta kai 81171, yayin da ake zaton wasu 132 da kamuwa da cutar a babban yankin kasar.

A wannan rana, karin mutum daya da aka tabbatar ya kamu da cutar, a birnin Wuhan dake lardin Hubei na kasar Sin yake. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China