Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya yi amai ya lashe kan yadda yake kiran COVID-19 da "cutar kasar Sin" a baya
2020-03-26 10:41:33        cri

Da alamun kwangaba-kwanbaya da ake samu tsakanin Sin da Amurka a 'yan kwanakin da suka gabata, ya sauya salo. Inda a ranar Litinin da ta gabata mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya bayyana cewa, matakan kasar Sin na yaki da COVID-19 "kusan a bayyane suke" idan aka kwatanta da yadda ta tunkari cututtukan da suka barke a baya. Shi ma shugaba Donald Trump, ya wallafa a shafinsa na Tewita a ranar Litinin din, inda ya kira cutar COVID-19 da cutar, maimakon yadda ya rika kiran cutar da sunan "cutar kasar Sin".

A yayin zantawarsa da gidan Talabijin na FOX a ranar Talata, Trump ya bayyana cewa, "bai kamata mu rika ruruta wannan batu ko mayar da shi wani babban batu ba," kuma ya yarda cewa, "Ina ganin na mayar da batun wani abu".

Hakika, wani abu ne. Tun lokacin da Trump ya fara kiran cutar da sunan "Cutar kasar Sin", akwai rahotanni da dama dake nuna yadda ake cin zarafin Sinawa da Sinawa Amurkawa a titunan kasar.

Gidan Talabijin na Fox ya ba da rahoton cewa, shugaba Trump yana fuskantar karin matsin lamba na siyasa daga Amurkawa masu tsatson Asiya dake da 'yancin kada kuri'a a jihohin kasar masu muhimmanci. Su ma 'yan Democrats da Republican na kokarin shiga sahu.

A bangaren kasa da kasa kuwa, wajibi ne a kyautata alaka da kasar Sin. Rahotanni na cewa, Amurka tana son shigo da abin rufe baki da hanci da ma kayayyakin kariya daga kasar Sin. A matsayinta na kasar dake kan gaba wajen sayen kayayyakin lafiya daga kasar Sin, kyautata dangataka da kasar abu ne mai muhimmanci a lokutan da ake fama da matsala

Sai dai kuma, matsalar ita ce, idan har matsalar lafiya da ta shafi jama'a ta dauki dogon lokaci, Trump ba zai ma yi tsammanin daidaita abubuwa da kasar don ya samu taimako har ma ya gyara raunin da ya yi mata ba. Samun magani da hana yaduwar cutar, ayyuka ne na dogon lokaci dake bukatar kayayyakin kiwon lafiya da na harhada magunguna, don haka, yin aiki tare yadda ya kamata tsakanin kasashen biyu, ya zama wajibi. Kiran cutar "Kwayar cutar kasar Sin" hakika ba zai haifar da da mai ido ba.

Idan aka yi la'akari da wadannan shawarwari, za a fahimci cewa, akwai bukatar gwamnatin Trump ta canja takunta. Ko dai ya gane kuskurensa ko ya dauki matakin da ya dace, wannan wani mataki ne na inganta alaka tsanakin kasashen biyu. Abu mai muhimmanci a halin yanzu, shi ne ya kamata duniya ta yi dogon tunani ta kalli lokacin da wannan cuta za ta kawo karshe. Dabara aka ce ta rage ga mai shiga rijiya. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China