Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi 'yan siyasar Amurka sun dauki matakan da suka dace don yakar cutar COVID-19
2020-03-20 11:09:27        cri

 

Kwanan baya, shugabannin Amurka sun kira COVID-19 da sunan "Kwayar cuta ta kasar Sin". Jama'ar kasar Amurka da kuma na sauran kasashen duniya, sun bayyana rashin jin dadi sosai kan wannan furuci. Ban da wannan kuma, saboda ganin matsaloli da dama da Amurka ke fuskanta wajen yaki, da kuma kandagarkin cutar, mutanen na ganin cewa, 'yan siyasar Amurka ba su dauki matakan da suka dace wajen yakar cutar ba.

Ran 11 ga wata, cutar ta kara kamari a Amurka, inda shugabannin Amurka suka yi ikirarin daukar matakai mafiya tsanani a tarihi don yakar cutar, kuma a ran 16 ga wata, an tambaye su mahangar su game da matakan da suka dauka, sai dai sun ba da maki 10, wato ba tsamani sun bayyana makin koli a fannin.

Ya zuwa yanzu dai, duk jihohi 50 da kuma yanki na musamman na Washington da Columbia,an samu bullar wannan cuta. Ko da yake, Amurka ta dauki matakin rage kudin ruwa, da manufar kudi mai sassauci, amma masu zuba jari ba su da isasshen kwarin gwiwa ga matakan da take dauka na yakar cutar, kuma kara faduwar farashin hannun jari a Amurka har sau 4 cikin kwanaki 10, na zama abin da ya fi jawo hankalin 'yan siyasar Amurka, saboda a ganinsu, farashin hannun jari shi ne ci gaban siyasa kadai a gare su, saboda matakin na da alaka matuka da kuri'un da za su samu yayin zabe.

Haka kuma ya bayyana tunanin 'yan siyasar Amurka na yaki da cutar, wato kudi ya fi rayuwar jama'a daraja.

S

aboda hakan, Amurka ta dauki mataki maras sahihanci don boye mataki maras inganci da ta dauka, na yakar cutar, da kuma rufe idanun jama'arta, sannan kuma da kawar da matsin lamba daga jama'a, ta kara wulakanta, da kuma shafa bakin fenti ga kasar Sin.

A hakika dai, gudun sauke nauyin dake wuya, da girman kai, ba za su iya taimakawa wajen tinkarar cutar ba ko kadan, kuma kalaman nuna bambancin launin fata, da tunanin mayar da wani saniyar ware, ba su da amfani wajen hadin kan kasa da kasa, wajen tinkarar matsalar kiwon lafiyar duniya.

Don haka kamata ya yi, 'yan siyasar Amurka sun dauki mataki dake da amfani ga lafiyar jama'ar kasar su, a gabar da ake yaki da wannan cuta mai tsanani ga dukkanin Bil Adama. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China