Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka na yunkurin bata alaka tsakanin Sin da sauran wasu kasashe
2020-03-24 20:57:09        cri

 

Bisa rahotanni gami da jawaban jami'an gwamnati da tashar intanet ta The Daily Beast ta Amurka ta wallafa a kwanan nan, an ce a lokacin da annobar cutar COVID-19 ke kara kamari a duk fadin duniya, manyan shugabannin Amurka na shirin bata sunan kasar Sin daga bangarori daban-daban, a wani kokari na rage matsin lambar siyasar da suke fuskanta, gami da samun karin kuri'u na goyon-baya. Amma irin wannan wayo da Amurka ta nuna, ya gamu da babban suka daga kasashen duniya.

Duba da gazawarsu, wajen dorawa kasar Sin laifin barkewar cutar a duniya, sai 'yan siyasar Amurka suka yi ta kokarin hura wutar rikici tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya.

 

 

A halin yanzu cutar COVID-19 na kara yin sauki a kasar Sin, kuma yayin da take ganin bayan cutar, gwamnatin Sin tana nuna kwazo wajen tallafawa sauran kasashen da suke da bukata, al'amarin da ya shaida cewa, Sin babbar kasa ce mai sauke nauyin dake wuyanta, wadda kuma ta samu babban yabo daga kasa da kasa, har ma akwai wasu 'yan kasar Italiya wadanda suka godewa kasar Sin, bisa taimakonta a shafin sada zumunta.

To sai dai kuma hakan ya janyo kishin wasu 'yan siyasa, gami da kafofin watsa labaran Amurka. A yayin da yake zantawa da gidan talabijin na FOX a kwanan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya rura wuta da gangan tsakanin kasar Sin da kasar Italiya, da ma tsakanin al'ummomin kasashen biyu. Kana, jaridar New York Times ta wallafa wani sharhi dake cewa, tallafin jinya da kasar Sin ta bawa sauran kasashe, ba tallafi ne zalla ba, wato ta gindaya wasu sharudda.

 

 

Wani mai amfani da intanet mai suna Santos, ya bayyana ra'ayinsa yana mai cewa, Amurka ta sanyawa Iran takunkumi, amma kasar Sin ta samar mata da tallafi. Amurka ta hana fasinjojin kasashen Turai su shiga kasar yawon bude ido, amma kasar Sin ta tura tawagar ma'aikatan jinya zuwa Italiya. Kasa da kasa za su fahimci wacece aminiyarsu ta kwarai.

Ko shakka ba bu, aika-aikar da wasu 'yan siyasar Amurka suke yi, na jirkita gaskiya, da hura wutar rashin fahimta ga dangantakar Sin da sauran kasashen duniya, sam ba zai ci nasara ba. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China