Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan Siyasar Amurka Masu Son Kai Suna Lalata Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Wajen Yaki Da Cutar COVID-19
2020-03-20 19:27:15        cri

A halin yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 ta bazu a kasashe da dama a duniya, kuma kasashe da dama sun ayyana dokar ta baci kan wannan cuta, don haka, akwai bukatar kasashen duniya su gaggauta hada kai don yaki da wannan annoba. Amma, wasu 'yan siyasar kasar Amurka masu son kai suna mayar kokarin hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar kandagarki da dakile yaduwar annoba baya.

A 'yan kwanakin da suka gabata, kamfanin gidan rediyo na Columbia na kasar Amurka ya bayar da rahoton cewa, domin inganta shirin "sayen kaya kirar Amurka", shugaban kwamitin cinikayya na kasar Amurka Peter Navarro ya bukaci shugabannin kasar Amurka da su ba da umurni ga masana'antun samar da kayayyakin jinya da su koma kasar Amurka, ta yadda kasar Amurka za ta iya rage dogaron da take kan kasashen waje.

Amma, an kafa tsarin masana'antun duniya bisa halayen da kasa da kasa suke ciki, wanda ya dace da bukatun kasuwanni da kamfanoni. Idan kasar Amurka ta dawo da masana'antun jinya zuwa kasarta ta hanyar daukar matakan siyasa, tabbas hakan zai haddasa asara ga kamfanonin da abin ya shafa. Ba shakka, shawarar da Peter Navarro ya baiwa Amurka, ba ta dace ba wajen yaki da cutar COVID-19.

Ban da haka kuma, a kwanakin baya jaridar New York Times ta wallafa wani rahoton cewa, gwamnatin kasar Amurka tana kokarin shawo kan wani kamfanin Jamus dake nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19 da ya kaura zuwa kasar Amurka. Haka kuma, rahoton ya ruwaito labarin wata kafar yada labarai ta kasar Jamus cewa, gwamnatin kasar Amurka tana da niyyar baiwa wannan kamfani dalar Amurka biliyan 1 domin samun cikakken iko kan amfani da allurar rigakafin, sabo da, tana fatan kasar Amurka ita kadai za ta iya samu da kuma amfani da allurar rigakafin cutar numfashi ta COVID-19. Dangane da wannan batu, kafofin yada labarai na kasar Jamus sun yi zargin cewa, shirin Amurka ya nuna mugun halinta

Yadda kasashen duniya suke yaki da cutar ya nuna halayensu da nauyin dake wuyansu. A yau Jumma'a, kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu sun kira taron ministocin harkokin wajen kasashensu kan batun cutar numfashi ta COVID-19 ta kafar bidiyo, wanda ya zama abin koyi ga kasa da kasa kan yadda za a karfafa hadin gwiwa wajen fuskantar manyan kalubale. Ya kuma nuna mana cewa, matakan da wasu 'yan siyasa na wata babbar kasa suka dauka, ba su dace da halin da muke ciki yanzu na hada kai wajen yaki da annobar ba, kuma ba su dace da ka'idar jin kai ba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China