Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wurare daban daban na Sin suna sa kaimi da a koma bakin aiki
2020-03-03 12:51:40        cri

A lokacin da ake dukufa wajen yin kandagarki ga yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin kasar Sin, wurare daban daban na kasar, suna daukar matakai wajen farfado da manyan shirye-shiryen gine-gine, da sa kaimi ga kamfanonin kasa da su koma bakin aiki.

Ya zuwa ranar 2 ga wata, an farfado da shirye-shirye guda 24 dake cikin shirye-shirye guda 25, na gini yankunan gasar wasannin motsa jiki na Olympics a lokacin sanyi dake tsakiyar birnin Beijing, da yankin karkara na Yanqing, na birnin Beijing, adadin da ya kai 96% cikin dukkanin shirye-shiryen da ake gina wa a yankunan. Kuma bisa shirin da aka tsara, za a kammala ayyukan gina dukkan dakunan gasar kafin karshen shekarar bana.

A ranar 2 ga wata kuma, an kaddamar da manyan shirye-shiryen ababan kamfanin mai na kasar Sin na Sinopec guda biyu a biranen Fuzhou, da Quanzhou na lardin Fujian, wadanda darajar su ta kai yuan sama da biliyan 60. Kana, bayan barkewar annobar, gwamnatin lardin Fujian ta samar da taimakon kudi na yuan miliyan 50 ga wasu manyan shirye-shirye bisa kasafin kudin sa.

A birnin Xiantao na lardin Hubei, wurin da aka fi samar da kayayyakin da ake bukata domin sarrafa abun rufe hanci da baki, da tufafin ba da kariya, an kafa tawagogin musamman guda 13, wadanda suke kula da ayyukan samar da kayayyakin rigakafi, da likitocin za su yi amfani da su, domin tabbatar da samar da isassun kayayyakin da masu aikin ceto suke bukata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China