Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na goyon bayan Masar a yaki da cutar COVID-19
2020-03-24 10:20:40        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, kasarsa na goyon bayan Masar a kokarin da take na yaki da cutar COVID-19, kuma a shirye take ta hada hannu da ita.

Xi Jinping, ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar, Abdel-Fattah al-Sisi.

Ya ce kasar Sin za ta hada hannu da sauran kasashen duniya wajen inganta hadin gwiwar kasa da kasa domin yaki da annobar, da shawo kan kalubale da barazanar da suke fuskanta da kare lafiyar al'ummar duniya da bisa ra'ayin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkan bil Adama.

Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take, ta gabatar da bayanai da matakanta na kandagarki da kula da marasa lafiya da sakamakon binciken lafiya ga Masar, da kuma samar mata kayayyakin kiwon lafiya domin taimakawa kokarinta na yaki da annobar.

A nasa bangaren, shugaba al-Sisi, ya ce Sin ta samu nasarori a yakin da take da cutar COVID-19, wanda ya nuna karfin shugabanci irin na shugaba Xi, da kuma goyon bayan da al'ummar Sinawa ke ba shi.

Ya ce Masar na yabawa taimakon kasar Sin, kuma tana da yakinin cewa, ta hanyar hada hannu wajen yaki da cutar, abota tsakanin kasashen biyu za ta kara karfi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China