Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwalliya ta fara biyan kudin sabulu wajen shawo kan cutar COVID-19 a Wuhan da ma Hubei
2020-02-21 11:21:04        cri
A wajen taron manema labarai da aka shirya jiya a birnin Wuhan na lardin Hubei, inda cutar numfashi ta COVID-19 ta fi kamari, memba a rukunin da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa lardin domin jagorantar ayyukan dakile cutar, kana mataimakin babban sakatare na majalisar gudanarwar kasar, Ding Xiangyang ya nuna cewa, kwalliya ta fara biyan kudin sabulu wajen shawo kan annobar a birnin Wuhan, da ma lardin Hubei baki daya, inda a cewarsa, idan aka ci gaba da daukar managartan matakai, adadin wadanda suka kamu da cutar zai dada raguwa.

Mista Ding ya bayyana cewa, an cimma wasu nasarori, a yayin da ake gudanar da ayyukan dakile yaduwar cutar COVID-19 a Wuhan, da ma Hubei a halin yanzu. Alal misali, sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar, gami da wadanda ake zato sun kamu da ita a birnin Wuhan, duk sun ragu daga sama da dubu 4 a kowace rana a tsakiyar watan Fabrairu, zuwa dubu 1 ko dubu 2 a kowace rana a halin yanzu. Kana kuma adadin mutanen da ake zato sun kamu da cutar, ya ragu daga matsayin koli wato sama da 18000 a farkon watan Fabrairu, zuwa kimanin dubu 2 a halin yanzu.

Har wa yau, Ding ya nuna cewa, yanzu haka akwai majinyata sama da dubu 30 a Wuhan, ciki har da wasu kananan yara, da wadanda ke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai da dama, wato akwai sauran rina a kaba game da ayyukan shawo kan cutar. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China