Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabbin yawan mutanen da suka warke daga annobar COVID-19 ya zarce wadanda suka kamu da cutar kwanaki uku a jere
2020-02-21 11:42:04        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Juma'a cewa yawan sabbin mutanen da suka warke daga cutar numfashi ta COVID-19 ya dara yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a cikin kwanaki uku a jere.

A ranar Alhamis majinyata 2,109 ne aka sallama daga asibitoci bayan sun warke daga cutar, wanda yayi matukar zarce adadin mutanen da suka kamu da cutar a wannan rana wato mutane 889, kamar yadda alkaluman hukumar lafiyar suka nuna.

Baki daya majinyata 18,264 ne suka warke daga annobar cutar numfashi ta COVID-19 ya zuwa ranar Alhamis kuma tuni an riga an sallame su daga asibitoci bayan sun warke.

Ranar Alhamis ce rana ta biyu a jere da aka samu sabbin yawan mutanen da suka kamu da annobar kasa da mutum 1,000 a nan kasar Sin.

Alkaluman hukumar lafiyar sun nuna cewa sabbin mutanen da suka warke daga annobar cutar numfashi ta COVID-19 a lardin Hubei da kuma babban birnin lardin wato Wuhan ya zarce yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar ya zuwa ranar Alhamis.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China