Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahukuntan kasar Sin sun jaddada bukatar daukar matakai daban daban na yaki da cutar COVID-19
2020-02-25 12:06:35        cri

Mahukuntan kasar Sin, sun jaddada bukatar daukar matakai daban-daban na kariya da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar.

Taron kwamitin yaki da cutar COVID-19 na kwamitin tsakiya na JKS da ya gudana jiya Litinin karkashin firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana cewa, ya kamata a dauki matakai bisa la'akari da yanayi daban daban na kowanne lardi, yayin yaki da cutar.

Taron ya kuma jaddada bukatar zage damtse wajen aiwatar da mabambantan ayyukan kariya da dakile yaduwar cutar da kuma komawa bakin aiki cikin tsanaki.

A cewar taron, kamata ya yi a yi kokarin gudanar da ayyuka da cimma burikan raya tattalin arziki da zamantakewa a bana.

Har ila yau, taron ya saurari rahotanni kan matakan kariya da dakile yaduwar cutar da gwamnatin tsakiya ta dauka a birnin Wuhan da lardin Hubei, da kuma abubuwan da ake bukata wajen yaki da cutar da kuma tsara yadda za a inganta tallafawa lardin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China