Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran za ta yi amfani da cibiyar kasuwanci wajen jinyar wadanda suka kamu da COVID-19
2020-03-23 09:11:59        cri

Rahotanni daga kasar Iran na cewa, kasar za ta yi amfani da katafaren cibiyar kasuwanci ta zamani, wajen kwantar da wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar na wucin gadi.

Kafar watsa labarai ta Press TV, ta bayyana cewa, cibiyar wadda ke yankin yammacin Tehran, babban birnin kasar, za a iya girka gadajen kwantar da marasa lafiya dubu 3 a cikinta. Kana fadin yankin kwantar da marasa lafiyan wanda a bayan ake baje kolin kayayyaki a cikinsa, ya kai sikwaya mita 45,000.

Tuni dai hukumomi suka ba da umarnin rufe cibiyoyin kasuwanci a Tehran, sakamakon kalubalen yaduwar COVID-19.

A jiya Lahadi, ma'aikatar lafiyar kasar Iran ta bayyana cewa, ya zuwa ranar Jumma'a mutane 21,638 ne suka kamu da cutar COVID-19, daga cikinsu mutane 1,685 sun mutu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China