Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda 'yan siyasar Amurka suka yi sakaci da aiki ne sanadin bazuwar cutar COVID-19 a Amurka da Turai
2020-03-23 20:08:55        cri

A ranar 20 ga wata, firaministan kasar Australiya Scott Morrison, ya bayyana wa manema labarai cewa, "akasarin masu cutar COVID-19 da aka gano a kasar sun zo ne daga kasar Amurka". Daga wannan rana da dare kuma, Australiya din ta haramtawa dukkanin baki shiga kasar.

A dukkan watan Faburairu, Amurka kusan ba ta dauki matakan da suka dace ba wajen dakile yaduwar cutar. A yayin da yanayin cutar ya kara tsananta, kuma al'ummar kasar suke ta kara bayyana rashin jin dadi, a ranar 13 ga wata ne Amurkar ta sanar da kafa dokar ta baci, tare da alkawarta daukar jerin matakai, alkawarin da kuma ba ta cika ba.

Babu isassun kayayyakin gwajin cutar, haka ma babu isassun gadaje da kayayyakin kandagarkin cutar a asibiti. A labarin da kafofin watsa labarai na kasar suka bayar, an ce, adadin masu cutar da ba a gano ba a kasar, ta yiwu ya ninka wadanda aka tabbatar sun kamu har sau 11.

Ya zuwa yanzu, yawan masu harbuwa da cutar da aka tabbatar a kasar ya zarce dubu 35, adadin da ya dora Amurkan a matsayi na uku a duniya. Duk da haka, gwamnatin kasar na tsayawa kan cewa, "sassa da dama na kasar ba su shiga hali mai tsanani ba", kuma suna ta dora laifin kan wasu.

Wani labarin da kafar yanar gizo ta "The Daily Beast" ta bayar ya nuna cewa, wani sakon da aka aikawa ma'aikatar harkokin waje ta kasar, ya bukaci jami'an kasar da su daidaita bakinsu, su dora laifin yaduwar cutar a kan kasar Sin. Sai dai masu bibbiyar shafukan yanar gizo sun gano makircinsu.

Daga bisani sannu sannu, Amurka ta rika sanya haramci tafiye-tafiye kan kasashen kawancenta na Turai. Kuma duk da cewa an rufe kofar shiga kasar, amma kofar fita daga kasar a bude take. Abin da ya sa kasashe kawayenta suke fama da barnar wannan cuta.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China