Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Magajin garin birnin New York ya zargi shugaba Trump da yin sakaci da aiki
2020-03-23 19:09:16        cri

A ranar 19 ga wata, magajin garin birnin New York Bill de Blasio, ya zargi gwamnatin Trump da yin sakaci da aiki, a maimakon ya tara albarkatun kasar baki daya don dakile yaduwar cutar COVID-19.

Mr. Bill de Blasio, ya soki shugaba Trump da cewa, "miliyoyin Amurkawa ba su gane me kake yi ba. A lokacin da kasarmu ta tsunduma cikin mawuyacin hali, ba ka gudanar da aikinka yadda ya kamata". Ya ce "A yayin da ake fuskantar barkewar annoba, kamata ya yi a hada karfin kowa da kowa, amma ba mu san dalilin da ya sa ka yi ta tsayawa kana kallo ba. Ga shi ka rasa damar ceton kasar Amurka."

Mr. Bill de Blasio ya kara da cewa, nan da sati biyu zuwa uku, kayayyakin jinya da ake bukata wajen shawo kan cutar za su kare, don haka ba yadda za a yi illa a hada karfi da bangaren sojojin kasar don biyan bukatun da ake da su. Sai dai har yanzu, rundunar sojan da ta fi karfi a duniya ba ta fara aiki ba.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China