Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tabbatar da sabbin mutane 39 sun kamu da cutar COVID-19 bayan sun taho da ita daga ketare
2020-03-23 10:26:12        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce ta samu rahoton cewa, a jiya Lahadi, sabbin mutane 39 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar, wadanda dukkansu suka taho da cutar daga ketare. Ya zuwa jiya Lahadi yawan wadanda suka taho da cutar daga ketare ya kai 353.

Haka kuma ya zuwa jiyan, jimilar mutane 5120 ne ke fama da cutar a babban yankin kasar Sin, yayin da mutane 72703 suka warke daga cutar, kuma aka sallame su daga asibiti, kana mutane 3270 sun rasa rayukansu. Jimillar wadanda suka kamu da cutar ta kai 81093, yayin da ake zaton wasu 136 da kamuwa da cutar a babban yankin kasar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China