Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hillary ta soki kalaman Trump tana mai cewa ra'ayin nuna bambancin launin fata ne
2020-03-20 11:12:46        cri

A ranar 16 ga watan nan, shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya kira cutar COVID-19 da sunan "kwayar cutar kasar Sin" a shafin sa na Twitter, ko da yake bangarori daban-daban na Amurka, da na ketare sun nuna matukar rashin jin dadi kan hakan.

A ranar 18 ga wata kuma, wadda ta yi takarar shugabancin kasar Amurka na shekarar 2016 tare da Donald Trump Madam Hillary Clinton, ta nuna cewa, maganar Trump babu komai a cikin ta sai ra'ayin nuna bambancin launin fata, da kuma yunkurin boye gazawar da yake cike a aikin yaki da kuma kandagarkin cutar COVID-19.

A wani sako da ta wallafa kan shafin ta na Twitter, Hillary ta ce, shugaba Trump na karkata zuwa ra'ayin nuna bambancin launin fata, don kawar da idanun jama'a daga tura da yake ci, wato bai dauki mataki da ya dace kan cutar cikin lokaci ba, bai kuma samar da isassun na'urorin gwada cutar ba, kana bai yi shiri tsaf don tinkarar wannan rikicin da ya dabaibaye dukkanin kasar a yanzu ba. A cewarta, Trump na tafka magudi, kuma bai kamata mutane da kuma dangoginsu su amince da shi ba.

Ranar 17 ga wata, jaridar New York Times ta wallafa wani labari dake cewa, a makwannin da suka gabata, Trump na yunkurin hana fidda labarai dangane da cutar a bayyane, da kuma yin dariya kan damuwa da aka yi game da cutar, ta yadda ya gaza dora muhimmanci kan kalubalolin da cutar za ta kawowa jama'a. Baya ga musanta tsananin cutar COVID-19 a cikin watanni biyu da suka gabata ba, Trump ya kuma zargi wadanda suke kokarin tinkarar cutar, tare kuma da baiwa jama'a labarai masu cike da kuskure dangane da cutar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China