Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana duba lafiyar mutane 13350 kan cutar COVID-19 a Amurka
2020-03-20 12:08:08        cri
A cikin kasa da sa'o'i 18 na ranar Alhamis, an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 3899 a Amurka, ya zuwa karfe 6 na yammacin jiya, gaba daya adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya kai 13350, kana adadin mutanen da suka rasu sakamakon cutar ya kai 188 a kasar, kamar yadda cibiyar kimiyya da fasaha ta (CSSE) dake jami'ar Johns Hopkins ta sanar.

Rahotanni na cewa, an tabbatar da yawan wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 kimanin 10995 a kasar Faransa zuwa yammacin ranar Alhamis, an samu yawan karin wadanda suka kamu da cutar kimanin 1861 idan an kwatanta da ranar Laraba, kana yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 372.

A kasar Italiya kuwa yawan wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 ya kai 41035 ya zuwa karfe 6:00 na yamma, agogon kasar a ranar Alhamis. Sabbin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 5322 cikin sa'o'i 24, baki daya mutane 3405 cutar ta kashe a kasar Italiya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China