Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karin mutane sun kamu da cutar COVID-19 a kasashen Turai
2020-03-21 17:00:39        cri
An samu karuwar wadanda ke kamuwa da cutar COVID-19 a kasashe daban daban dake nahiyar Turai a jiya Juma'a.

A kasar Italiya, an samu sabbin mutane 5,986 da suka kamu da cutar, lamarin da ya sa daukacin mutanen da cutar ta harba a kasar suka kai 47,021. Cikinsu wasu 4,032 sun mutu, yayin da wasu 5,129 suka warke.

A nata bangare, ma'aikatar lafiya ta Birtaniya, ta bayyana a jiya Juma'a cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ya karu da 714, inda jimilarsu baki daya ta cimma 3,983, yayin da wasu 177 suka mutu.

A jiya da daddare ne kuma, firaministan Birtaniyar, Boris Johnson ya sanar da umarnin gwamnati, na bukatar dukkan dakunan cin abinci da na nishadi a kasar, su dakatar da ayyukansu nan take.

A kasar Faransa ma, Jerome Salomon, babban darektan hukumar lafiya ta kasar, ya bayyana a jiya cewa, wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar sun kai 12,612, adadin da ya karu da 1,617, idan an kwatanta da na ranar Alhamis. Kana yawan mutanen da suka mutu ya kai 450, wanda ya karu da 78.

Ban da haka Florence Parly, ministar tsaron kasar Faransa, ta sanar a jiya cewa, sojojin ruwan kasar za su tura wani jirgin ruwan yaki don kwashe wadanda suka kamu da cutar COVID-19, dake cikin yanayi mai tsanani, daga tsibirin Corsica na kasar, zuwa asibitocin dake da muhallin jinyarsu. Ban da haka kuma, an ce a Mulhouse dake gabashin kasar, an fara gina wani asibiti na wucin gadi, wanda ake sa ran fara amfani da shi a ranar 26 ga watan da muke ciki. Wannan sabon asibitin zai samar da gadaje 30 don kwantar da wadanda ke cikin yanayi mai tsanani. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China