![]() |
|
2020-03-19 15:32:52 cri |
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya sanar a ranar Laraba cewa, kashi 80 bisa 100 na yawan mutanen da suka kamu da cutar a duk fadin duniya daga shiyyoyi biyu ne, wato kasashen yammacin tekun Pacific da nahiyar Turai.
A bisa alkaluman hukumar ta WHO, adadin mutanen da suka kamu da cutar daga wajen kasar Sin ya kai 112,878 ya zuwa safiyar ranar Laraba.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China