Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afitka ta kudu ya nemi goyon bayan jam'iyyun siyasan kasar don yakar COVID-19
2020-03-18 19:33:42        cri
Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya bukaci dukkan jam'iyyun siyasun kasar, da su hada kai wajen yaki da cutar COVID-19.

Ramaphosa ya yi wannan kira ne Larabar nan, bayan ganawa da shugabannin jam'iyyun siyasa a majalisar dokokin kasar, don tattauna matakan da kasar ke dauka game da yadda cutar COVID-19 ke yaduwa. Yana mai cewa, idan ana batun COVID-19, babu maganar surutai da bambancin siyasa .

Kalaman shugaban na zuwa ne, bayan da aka tabbatar da mutane 116 sun kamu da cutar a kasar, yayin da cutar ke kara yaduwa a cikin kasar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China