Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 116 sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka
2020-03-12 11:50:03        cri

Wani sabon rahoto da aka fitar na cewa, mutane 116 ne aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar Afirka baki daya, wadanda suka shafi kasashe 12, ciki har da mutane biyu a kasar Nijeriya.

A kokarin da ake na yakar cutar, kasashen duniya da dama, ciki har da kasar Amurka da sauransu, sun kara tsaurara matakan takaita shiga kasashensu da sauran matakan gargadi kan cutar.

Jiya Laraba, shugaban kasarAmurka Donald Trump ya sanar da cewa, daga gobe Jumma'a 13 ga wata, kasarsa za ta hana dukkan 'yan kasashen Turai, ban da kasar Burtaniya, daga shiga kasar Amurka, cikin kwanaki 30 masu zuwa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China