Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afrika 40 sun tabbatar da rahoton kamuwa da COVID-19 kimanin 1,114
2020-03-22 16:31:14        cri
Adadin mutane da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya karu a Afrika zuwa 1,114 yayin da aka samu rahoton bullar cutar a kasashe 40 na Afrika ya zuwa ranar Asabar, cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika wato (Africa CDC) ta tabbatar da hakan a jiya Asabar.

Ahmed Ogwell, mataimakin daraktan cibiyar ta Africa CDC, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa bayan samun rahoton mutane 1,114 da suka kamu da cutar a kasashen Afrika 40, an kuma samu hasarar rayuka kimanin 28 a nahiyar ya zuwa ranar Asabar.

Ogwell ya nanata cewa, yayin da ake kan mataki na farko na bazuwar cutar ta COVID-19 a nahiyar, adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a nahiyar ya tabbatar da cewa cutar ta zama annobar da ke bukatar daukar matakan gaggawa domin dakile yaduwarta.

Alkaluman da Africa CDC ta fitar ya nuna cewa, kasashen Afrika da annobar COVID-19 ta fi kamari sun hada da Masar da aka samu yawan mutane 285, da Afrika ta kudu 240, da Algeria 102 ya zuwa safiyar ranar Asabar. Afrika ta kudu da Algeria, da aka samu rahoton kamuwa da cutar COVID-19 kimanin 202 da kuma 82 da safiyar ranar Asabar, an kuma samu rahoton sabbin mutanen da suka kamu da cutar a kasashen biyu kimanin 38 da kuma 20 ya zuwa yammacin wannan rana.(Ahmad Inuwa Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China