Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AFRAA na kira da a bullo da manufar da za ta baiwa kamfanonin jiragen saman nahiyar Afirka damar yin takara da takwarorinsu na ketare
2020-03-11 11:16:39        cri
Kungiyar zirga-zirgar jiragen sama ta Afirka, wato AFRAA a takaice, ta yi kira da a fadada manufar kungiyar nahiyar, ta yadda kamfanonin jiragen saman nahiyar za su iya yin takara da takwarorinsu na ketare.

Babban sakataren kungiyar Abderahmane Berthe, shi ne ya bayyana haka ga taron manema labarai a Nairobin Kenya, yana mai cewa a cikin shekaru ashirin da suka gabata, yawan kason da kamfanonin jiragen saman nahiyar suka samu a cikin kasuwa, ya ci gaba da raguwa, inda kamfanonin jiragen saman kasa da kasa suka mamaye kasuwan zirga-zirgar jiragen saman na Afirka.

Ya ce, a halin yanzu, kamfanonin jiragen saman Afirka suna samar da hidima ga kaso 20 cikin 100 kawai na fasinjojin dake kai koma tsakanin Afirka da sauran sassa na duniya. Berthe ya ce, muddin ana son shawo kan wannan matsala, nahiyar ta Afirka tana bukatar manufar zirga-zirgar jiragen sama a mataki na kungiyar tarayyar Afirka. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China