Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin Kai Ya Kasance Mataki Mai Karfi Wajen Yaki Da Cutar COVID 19
2020-02-23 20:22:59        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa sakon da Bill Gates, shugaban asusuan Gates da Melinda, ya aiko masa kwanan baya cewa, dukkan bil'adama na cikin al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya. A cikin sakon da Bill Gates ya aikewa shugaba Xi ya jinjinawa matakan da gwamnatin Sin da jama'arta suke dauka.

To, mene ne al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkan Bil Adama? Ana iya fahimtar wannan batu sosai saboda barkewar wannan annoba. Cuta na iya yaduwa zuwa ko ina a duniya, hanya daya tilo da ya kamata Bil Adama za su bi ita ce: Hadin kansu.

Sin tana namijin kokarin aiwatar da harkokin kanta don bada tabbaci ga rayuwar jama'arta da ma al'ummar duniya, da taka rawa gwargwadon karfinta ga sha'anin lafiyar jama'ar duniya, saboda ganin nagartattu da tsauraran matakan da take dauka na tinkarar cutar, da kuma ci gaban da take samu na gudanar da aikin kandagarki, har ma da gabatarwa WHO da dai sauran kasashe masu nasaba sakonni a bayyane, don baiwa sauran kasashen isashen lokacin yin kandagarki.

Har illa yau, jami'an kasashe ko kungiyoyin kasa da kasa 160 sun aikawa gwamnatin kasar Sin sako ko buga waya don nuna goyon bayansu, har ma kasashe da kungiyoyi daban-daban fiye da 30 sun baiwa kasar Sin tallafi, sannan kuma, kamfanonin ketare dake kasar Sin sun bada tallafin kayayyaki, duk matakan dake bayyana cewa, al'ummar duniya suna daukar matakan da suka dace don marawa kasar Sin baya da tinkarar wannan annoba tare.

A hakika dai, kamata ya yi a yi watsi da tunanin katse hulda da kasar Sin ko tunani na wani bangare daya dake samun riba, ta yadda wani bangare na daban tilas ya yi hasara da tunanin mayar da wani saniyar ware, don cimma nasarar yaki da wannan cuta ko hana yaduwarta zuwa sauran sassan duniya.

"Hadin kai ya kasance mataki mai karfi wajen yaki da cutar COVID-19", wata jimla da shugaba Xi Jinping ya rubuta a cikin wasikar maida martani ga wasikar da Bill Gates ya rubuta masa, ta baiwa kasashen duniya wata hanya da ta dace da za a bi wajen tinkarar kalubale cikin hadin kai. (Mai fassarawa: Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China