Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar kare muradun Amurka da farko ta rage amfanin kasashen yammacin duniya
2020-02-16 20:49:15        cri

A gun taron Munich kan harkokin tsaro da aka gudanar a ranar 14 ga wannan wata, shugabar majalisar wakilai ta kasar Amurka Nancy Pelosi ta zargi Sin da ta raya tsarinta na fasahar sadarwa ta hanyar kamfanin Huawei. Mataimakiyar direktan kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma tsohuwar mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar Sin Fu Ying ta mayar da martani da Turanci nan da nan, inda ta yi nuni da cewa, bayan da Sin ta bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, an shigar da fasahohin kasashen yammacin duniya iri daban daban, kamar fasahar 1G, da 2G, da 3G, da 4G da sauransu. Kana kamfanonin Microsoft, da IBM, da Amazon sun gudanar da ayyukansu da dama a kasar Sin. Ko Pelosi ta yi tsammani tsarin demokuradiyyar ba shi da inganci ne, shin wace barazana kamfanin fasaha kamar Huawei zai kawo gare su?

Bayan da Fu Ying ta bayyana hakan, masu kallo a wurin sun yi tafi da nuna amincewa gare ta sosai. Pelosi ta ce kamfanonin Sin kamar Huawei ba su yi ciniki cikin 'yanci ba. Amma ka'idar nuna rashin bambanci tana daya daga cikin ka'idojin da kamfanoni masu samun 'yanci suke bi. Wasu 'yan siyasa kamar Pelosi sun sabawa wannan ka'ida. Game da ra'ayin Pelosi, kasashen Birtaniya da Jamus ba su amince da ita ba, dukkansu suna son samar da yanayi cikin adalci ga kamfanonin sauran kasashen duniya, ciki har da kamfanin Huawei.

Taken taron Munich na wannan karo shi ne "Amfanin kasashen yammacin duniya ya ragu". An tsara wannan take ne domin kasar Amurka ta gudanar da ayyukan bisa manufar kare muradunta da farko. Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi nuni da cewa, dalilin da ya sa Amurka ta sake samun karfi domin ta lalata moriyar kawancenta.

Bisa labarin da jaridar The Washington Post ta bayar a kwanakin baya, an ce, kamfanin Crypto AG mai samar da na'urorin kiyaye asiri dake karkashin jagorancin hukumar leken asiri ta kasar Amurka ya samarwa kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya hanyoyin leken asiri ga E-mail na sirri da aka tura a tsakanin kasa da kasa. Wannan shiri mai suna Rubicon yana shafar kasashe fiye da 120 a duniya. Wannan aiki na sa ido ga dukkan kasashen duniya ya yi bambamci sosai da ra'ayin raya kamfanoni masu 'yanci da Pelosi ta gabatar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China