Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mugun nufin da ake da shi yayin da ake yada jita-jita kan cutar covid-19
2020-02-22 21:15:56        cri

A ranar 21 ga wata, agogon Rasha, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Rasha ya watsa labari, inda ya yi karin haske kan jita-jitar da aka yada cewa, wai Rasha na ganin dan Adam ne ya hada kwayar cutar COVID-19. Haka kuma bangaren Rasha shi ma ya ba da amsar cewa, ma'aikatar kiwon lafiyarsa ba ta taba nuna hakan ba, a cikin dabarar wucin gadi ta maganin cutar da tabbatar da ita da ma jiyyarta.

Yayin da ake kokarin yaki da cutar COVID-19, masu adawa da kasar Sin na yammacin duniya sun sha yada jita-jita kan dalilin da ya haddasa bullowar cutar, da ma shafa wa kasar Sin bakin fenti kan kokarin da ta ke yi na yaki da cutar.

A idanun wadannan 'yan adawa, bai kamata a tausayawa Sinawa ba, a maimakon haka suna amfani da wannan damar wajen kulla makircinsu. A wani bangare, suna yunkurin kawo wa mutane rudanni ta hanyar amfani da jita-jitar, har ma da kawo cikas ga hadin gwiwar Sin da hukumar lafiya ta duniya WHO, da ma sauran kasashe. A wani bangaren kuwa, ra'ayin tsayawa kan takara ba tare da hadin kai ko kadan ba da suke dauka, hanya ce ta neman cimma makarkashiyarsu a siyasance.

Ban da wannan kuma, suna da wani boyayyen dalilin, wato suna kishin yadda kasar Sin ke iya tattara dukkan Sinawa wajen yaki da cutar cikin yakini, baya ga kin amincewa da gazawar tsarin siyasarsu a wannan fannin. Sakamakon hakan, suna gaggawar yada jita jita ba tare da hujja ko dalili ba.

A 'yan kwanakin nan kuma, hukumar WHO da sassan kimiyya na duniya suna ta tsokaci don goyawa kasar Sin baya kan kokarinta na yaki da cutar. Kamar yadda suka ce, ana bukatar kimiyya, hankali, da ma hadin gwiwa wajen cimma burin ganin bayan cutar, a maimakon jahilci, jita-jita, da ma nuna bambanci.

Kamar yadda shahararren masanin ilmin siyasa na kasar Rasha KJ Noh ya fada, duk wanda ya tada kurar kiyayya kan wata kasa, to kaikayi zai koma kan mashekiya.(Kande Gao, ma'aikaciyar sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China