Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ce Sin za ta taimakawa Spaniya don yaki da cutar COVID-19
2020-03-18 11:09:28        cri

Gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakar kokarinta wajen samar da tallafi da kuma taimakawa kasar Spaniya don yaki da cutar numfashi ta COVID-19, shugaban kasar Sin Xi Jinping shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin zantawa ta wayar tarho da firaministan Spaniya Pedro Sanchez da yammacin ranar Talata.

Xi ya nanata cewa sakamakon aikin tukuru da aka gudanar a duk fadin kasar Sin, matakan da kasar ta dauka na yin kandagarki da kuma dakile cutar sun haifar da kyakkyawan sakamako, kuma kasar Sin ta fice daga cikin matsanancin halin da ta shiga a sanadiyyar barkewar cutar.

A halin yanzu annobar cutar tana cigaba da bazuwa a kasashen duniya masu yawa, shugaba Xi ya ce kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da kasa da kasa domin tallafawa sauran kasashen duniya don yaki da cutar gwargwadon karfinta.

Shugaban ya bayyana kwarin gwiwa cewa idan kasashen duniya suka yi hadin gwiwa da yin aiki tare wajen tunkarar annobar, kuma aka jure dukkan wahalhalun dake tattare da ibtila'in annobar aka dauki kwararan matakai a bayyane da yin hadin gwiwa tare, za'a cimma nasarar ceto tsaron lafiyar kasa da kasa.

A nasa bangaren, Sanchez ya ce halin da ake ciki na barkewar cutar COVID-19 a kasar Spaniya ya tsananta matuka, jama'ar kasar Spaniya suna matukar farin ciki da godiya bisa taimakon da kasar Sin ta ba su a lokacin da ya dace na kayayyakin kiwon lafiya da suke bukata, wanda a cewarsa hakan ya kara bayyana yadda kasar Sin ke nuna kauna ga jama'ar kasar Spaniya. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China